Acts 9

1Amma Shawulu, ya cigaba da maganganun tsoratarwa har ma da na kisa ga almajiran Ubangiji, ya tafi wurin babban firist 2kuma ya roke shi wasiku zuwaga majami’un da ke Dimashku, domin idan ya sami wani da ke na wannan hanya, maza ko mata, ya kawo su Urushalima a daure.

3Yayin da yana tafiya, ya kasance da ya iso kusa da Dimashku, nan da nan sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi; 4Sai ya fadi a kasa kuma yaji wata murya na ce da shi, ‘’Shawulu, Shawulu, me yasa kake tsananta mani?‘’

5Shawulu ya amsa, ‘’Wanene kai, Ubangiji?‘’ Ubangiji ya ce, ‘’Nine Yesu wanda kake tsanantawa; 6amma ka tashi, ka shiga cikin birnin, kuma za a gaya maka abinda lallai ne kayi. 7Mutanen da ke tafiya tare da Shawulu suka tsaya shiru sun rasa abin fada, suna sauraron muryar, amma ba su ga kowa ba.

8Shawulu ya tashi daga kasa, kuma daga ya bude idanunsa, baya ganin komai; sai suka kama hannuwansa suka yi masa jagora suka kawo shi cikin birnin Dimashku. 9Har kwana uku ba ya kallo, kuma ba ya ci balle sha.

10Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya; sai Ubangiji ya yi magana da shi cikin wahayi, ya ce, ‘‘Hananiya.‘’ Sai ya ce, ‘’Duba, gani nan Ubangiji.‘’ 11Ubangiji ya ce masa, ‘’Tashi, ka tafi titin da ake kira Mikakke, kuma a gidan wani mai suna Yahuza ka tambaya mutum daga Tarsus mai suna Shawulu; gama yana addu’a; 12kuma ya gani cikin wahayi mutum mai suna Hananiya na shigowa kuma ya daura masa hannu, domin idanunsa su bude.‘’

13Amma Hananiya ya amsa, ‘’Ubangiji, na ji labari daga wurin mutane da yawa game da mutumin nan, da irin muguntar da ya aikata ga tsarkakan mutanenka da ke Urushalima. 14An bashi izini daga babban firist domin ya kama dukan wanda ke kira bisa sunanka.‘’ 15Amma Ubangiji ya ce masa, ‘’Jeka, gama shi zababben kayan aiki na ne, wanda zai yada sunana ga al’ummai da sarakuna da ‘ya’yan Isra’ila; 16Domin zan nuna masa irin wahalar da zai sha sabo da sunana.‘’

17Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Ya dora masa hannu a kai, ya ce, ‘‘Dan’uwa Shawulu, Ubangiji Yesu, wanda ya bayyana a gareka a hanya sa’adda kake zuwa, ya aiko ni domin ka sami ganin gari ka kuma cika da Ruhu Mai Tsarki.‘’ 18Nan take wani abu kamar bawo ya fado daga idanun Shawulu, kuma ya sami ganin gari; ya tashi aka yi masa baftisma; 19kuma ya ci abinci sai aka karfafa shi. Ya zauna tare da almajirai a Dimashku kwanaki da yawa.

20Nan take ya fara shellar Yesu cikin haikali, yana cewa shine dan Allah. 21Dukan wadanda suka saurare shi suka yi mamaki suka ce ‘’Ba wannan mutumin ne yake hallaka mutanen Urushalima da ke kira bisa ga wannan suna ba? Ya kuma zo nan domin ya ba da su a daure ga manyan firistoci.‘’ 22Amma Shawulu kuwa ya sami iko sosai, kuma yana haddasa damuwa tare da rinjaya tsakanin Yahudawan dake zama a Dimashku ta wurin tabbatar da Yesu shine Almasihu.

23Bayan kwanaki da yawa, sai Yahudawan suka yi shiri domin su kashe shi. 24Amma shirin su ya zama sananne ga Shawulu. Suna fakkon sa ta wurin tsaron kofar birnin dare da rana domin su kashe shi. 25Amma da tsakar dare almajiransa suka daukeshi a kwando, suka zurara shi ta katanga.

26Sa’adda ya zo Urushalima, Shawulu ya yi niyyar hada kai da almajirai, amma dukansu suna tsoronsa, domin ba su yarda cewa shima ya zama almajiri ba. 27Amma Barnaba ya dauke shi ya kawo shi wurin manzannin. Ya kuwa gaya musu yadda Shawulu ya sadu da Ubangiji a hanya, har Ubangiji ya yi magana da shi, kuma yadda Shawulu ya yi wa’azi cikin sunan Yesu gabagadi a Dimashku.

28Ya sadu da su lokacin shigar su da fitar su a Urushalima. Ya yi wa’azi gabagadi cikin sunan Ubangiji Yesu 29kuma yana muhawara da Yahudawan Helenanci; amma sun ci gaba da kokarin kashe shi. 30Da ‘yan’uwa suka gane haka, sai suka kawo shi Kaisariya, suka kuwa tura shi zuwa Tarsus.

31Sa’annan iklisiya dake dukan kasar Yahudiya, Galili da kuma Samariya suka sami salama da kuma ginuwa; suka kuwa ci gaba da tafiya cikin tsoron Ubangiji, da kuma ta’aziyar Ruhu Mai Tsarki, iklisiyar kuwa ta karu da yawan mutane. 32Har ta kai, yayin da Bitrus ya zaga dukan yankin kasar, ya dawo wurin masu bi dake zama a garin Lidda.

33A can kuwa ya sami wani mutum mai suna Iniyasu, wanda yake shanyayye ne, yana kwance har tsawon shekara takwas a kan gado. 34Bitrus ya ce masa, ‘’Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka nade shimfidarka.‘’ Nan take sai ya mike. 35Sai duk mazauna kasar Lidda da kasar Sarona suka ga mutumin, suka kuma juyo ga Ubangiji.

36Yanzu kuwa a Yafa akwai wata almajira, mai suna Tabita, ma’ana ‘‘Dokas.‘’ Wannan matar kuwa tana chike da ayyukan nagarta da halin tausayi da take yi ga mabukata. 37Ya kai ga cewa a kwanakin can ta yi rashin lafiya har ta mutu; da suka wanke gawar ta suka kwantar da ita a bene.

38Da shike Lidda na kusa da Yafa, almajiran kuma sun ji cewa Bitrus yana can, suka aika mutane biyu wurinsa. Suna rokansa, ‘’Ka zo garemu ba tare da jinkiri ba.‘’ 39Bitrus ya tashi ya tafi da su, da isowar sa, suka kai shi benen. Sai dukan gwamrayen suka tsaya kusa da shi suna kuka, sai suka dauko riguna da sutura da Dokas ta dinka lokacin da take tare da su.

40Bitrus ya fitar da su duka daga cikin dakin, ya durkusa, ya yi addu’a; sai, ya juya wurin gawar, ya ce, ‘’Tabita, tashi.‘’ Ta bude idanunta, da ta ga Bitrus ta zauna, 41Bitrus kuwa ya mika hannunsa ya tashe ta; sa’annan ya kira masu bi da gwamrayen, ya mika ta a raye garesu. 42Wannan al’amari ya zama sananne cikin dukan Yafa, kuma mutane da yawa suka bada gaskiya ga Ubangiji. Ya kasance, cewa, Bitrus ya zauna kwanaki da dama a Yafa tare da wani mutum mai suna Saminu, majemi.

43

Copyright information for HauULB